Ƴan bindiga sun halaka ƴan sakai mutum tara a wani mummunan kwanton ɓauna da suka yi musu a jihar BauchiƳan sakan dai sun fita aikin sintiri ne domin kakkaɓe miyagun ƴan bindiga lokacin da lamarin ya aukuA yayin kwanton ɓaunan dai, rayukan ƴan sakai mutum tara ne suka salwanta ya yin da wasu da dama suka samu raunikaJihar Bauchi - Ƴan bindiga sun kashe ƴan sakai mutum tara waɗanda aka fi sani Ƴan Ba Beli a ƙauyen Gamji da ke ƙaramar hukumar Ningi ta jihar Bauchi. Wani ɗan kungiyar ƴan sakan da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a lokacin da ƴan sakan suka fita sintiri, cewar rahoton Daily Trust. Yan bindiga sun halaka yan sakai a jihar Bauchi Hoto: Theguardian.comAsali: UGCMajiyar ta bayyana cewa ƴan bindigan sun yi wa tawagar ƴan sakan kwanton ɓauna inda suka kashe mutum tara tare da raunata wasu da dama. Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 3 a BenueA wani labarin na daban kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai wani mummunan hari a ƙauyen Imaton na ƙaramar hukumar Logo ta jihar Benue. Ƴan bindigan waɗanda suka addabi mutanen yankin da kai hare-haren ta'addanci, sun salwantar da rayukan mutum uku a sabon harin da suka kai.
Source: The Guardian October 17, 2023 16:42 UTC